Kalaman Soyayya Masu Dadi da Ratsa jiki:- Soyayya

Rarraba

Kalaman Soyayya Masu Dadi da Ratsa jiki,

Karanta: Kalaman Soyayya Masu Dadi da Ratsa jiki,

Shin kana cikin Samari Masu neman Budurwa wadda zasu aura? Ko kana shan Wahala Wurin tsayar da budurwa da kake so ka aura,?

Nasan Soyayya itace take Ranka Wannan yasa kake ƙaranta Wannan Rubutun.

To inda Kana Soyayya kuma kana cikin Samari Masu yin Soyayya Yana da kyau Duk Saurayi Yasan Cewa Budurwa Sai da Kalaman Soyayya

Idan baka iya yimata Kalaman Soyayya to za,a Barka A baya Wurin Soyayya, Wannan Ita Magana ta Gaskiya,

Domin sau dadama ansha amshe ma saurayi Budurwa ta Dalilin rashin iya kalaman soyayya.

Wannan ne yasa Muka Tace, Muka Darje, Muka tsara muku Kalaman Soyayya Masu Dadi da Ratsa jikin Masoya.

Gasu a nan kasa Asha Karatu Lafiya.

Abubuwa kaɗan ne suke da daraja a wurina cikin wannan duniyar, ɗaya daga cikin su shine Murmushi ki, my priceless gift.

Gari ya Waye, sabuwar rana ta fara, Ina Farin ciki da Nishadi saboda ina da ke a cikin rayuwata.

Ina jin Soyayyar ki Wata Kyauta ce agareni da ban taba samun kyauta irin ta ba a rayuwata, my super lady.

Na dade ina kallon taurarin samaniya yayinda naga wacce tafi kowacce haske, saina naga bakowa bace nike ganiba sai ke masoyiyata! So gamon jinine, haqiqa sonki ya zamo jinin jikina!

Ki kwantar da hankalinki masoyiyata babu
wata a zuciyata sai ke kadai!

Congrats to me, saboda na Samu Mafi kyawu, Kulawa da Yarinyar da take Saurin Fahimta ta, kuma kece, my love

Yarda da amincewarki gareni, sune zasu
tabbatar da soyayyarki ta gaskiya a gareni!

Yau nayi mafarki, Kin kawo mini ruwa mai sanyi tare da wani a hannun ki, wannan abun kuwa shine soyayya ta dana baki, ki riƙe shi kada ki sake.

Farin ciki baya dorewa a rayuwa sai tare da bakin ciki, dan haka kowane hali nike bazan taba mantawa dake ba masoyiyata!

Da Farko Ina Miki Sallama Irin Wacce Na Saba Miki a Kullum, Sannan Ina Miki fatan Alkhairi irin wanda na saba a kullum, kin tashi lafiya, Ya zuciyar ki take? Ta kasance lafiya, ko ta kasance kullum cikin tinani na? Ba sai kin bani amsa ba, bugun zuciyarki zai sanar dani.

Nakan raba dare ina mai roqon Allah don
neman biyan buqata, ko kinsan kece abu na farko da nike roqo samu!

Gari ya waye, hasken rana ya fito, nima kuma na fito domin cigaba da noma gonar soyayyarki dana saba a Kullum, ina fatan irin dake Zuciyar ki ya kasance dai dai da irin wanda nake shukawa, Domin samun yabanya mai albarka tsakani na dake, Soyayyar ki tasa ni yin hudar da ba tare da garma ba.

Kamar yadda kowacce bishiya kanyi rassa a sama, kuma tayi saiwa a qasa, haka sonki ya mamaye dukkan jikina, idan na kalleki sai nayi farin ciki, idan naji tattausan muryarki, sai nishadi da walwala tare da annashuwa gami da farin ciki su mamaye zuciyata!

Akan ki zan iya komai banda Mutuwa, domin ina Son na kasance dake har abada, Nayi rayuwa dake mai kyau mai tsafta, Ina Miki barka da safiya Tare da fatan Zaki Wuni lafiya tare da farin ciki, Ki sani Ina Tare dake kuma Ina Qaunarki.

Abun da na ke ji a dangane da ke gaskiya ne kema na san kin san da haka cewa ina son ki, a duk lokacin da kika bar ni ba zan iya motsawa ko da nan da can ba, wannan shi ne abun da zai faru da ni a duk lokacin da na rasa ki.

Koma Karanta:  Halayya 4 Da Mata Sukafi Tsana a Wurin Maza

Zuciya Tana son mai kyautata mata, ni kuma tawa zuciyar ke take son ki kyautata mata, ki bata farin ciki. Duk safiya Murmushinki ya ta dani daga bacci.

Gimbiyar Mata Sarauniyar Zuciyata Kin tashi Lafiya, Ina Fata kin tashi cikin farin ciki irin wanda ke saka Annashuwa, Duk da Kasancewar ki a nesa dani, Amma zuciyata ta Kasance a Kusa dake, naso ace duk safiya idanu na dake zasuyi tozali, naso ace Kece mai tashina daga dogon mafarkin dana fada, naso ace Sassanyar Muryarki Mai Zakin Nan Ce Farkon saurarona a ko wace safiya.

SO tamkar wata sarkar zinari ce da ta d’aure zuciyoyin mu a waje guda, a dukkan lokacin da kika tsinka waccan sarka tofa ki tabbatar da cewa tamkar kin kore farin ciki ne daga cikin zuciya ta.

Sahibata, Na Gwammaci Na Qare Rayuwata baidaya tare dake, Akan Na Kasance Kullum Cikin Kadai ci, yau wata rana ce sabuwa, kuma ina fatan ta Kasance Mai dadi agaremu Baki Daya. Ina Fatan Kina Lfy?

ina son ka, me ya sanya ka ke yin
kokwanto a bisa kalmar so da na furta a gare ka?

Kin Sakaltani Da Kulawarki, tare da Tausayawarki, gashi yanxu Bana iya wuni ban ganki ba, Zuciyata tayi sabo dake irin sabon da bazan iya yankeshi da takobi ba,


Tabbas kaine mutum na farko da haduwa da shi ya kore min bakin ciki, ya wanzar da farin ciki a zuciya ta ya yalwata murmushi a saman fuska ta hakane dalilin da ya sanya na ke kiran ka da
SADAUKI.

Babban Burina a Duniya Shine ki kasance tawa, nima na kasance naki na har abada, Wannan ma kawai ya ishen rayuwa My love!

Salim, ka yi nasara ka yi nasarar jan ra’ayin soyayya ta a kan ka kaine na mallakawa linzamin zuciyata, kaine mutum na farko da na taba furtawa kalmar SO kuma a yanzuma zan
kara mai-maitawa a gare ka ina son ka.

Ganin Kyakkyawar Fuskar ko wace safiya Shine dalilin Farin cikina a wannan ranar, Domin Kece Hasken Rayuwata.

Babban burina naga bayyanar fitar murmushi akan wannan kyakkyawar fuskar taki,yakuma zamana nine sanadin hakan.

Ko wace safiyata Farin Ciki ne, saboda wata dama ce ta sake ganin Murmushinki, Da idanuwan ki masu daukar hankalina, da Kyakkyawar Fuskarkia mai sakan Murmushi, tare da sauraron muryarki mai sani Cikin kogon tinanin ki.

banason Allah yakawo lokacinda zaki fushi dani sosai,domin kaina bazai iya daukaba.

Nidai banzo gareki da wasa ko Soyayyar qarya ba, da gaske nake, sannan domin Tabbatar miki hakan zanso ki bani amsa, sannan ki bani dama nazo mu gana koda sau daya ne.

hakika Allah ya wadataki da abinda mata dayawa suke nema sun rasa.
Bashakka mata irinku kadanne, ke, da ace na’iya rubuta labari,to da’akan kyawun fuskarki zan rubuta littafin mai suna KYAUTA DAGA ALLAH.

Nidai ina Sonki, Ina Qaunarki, Soyayyar ta jima a zuciyata, nayi zurfin ciki ne saboda kada na bata miki rai ko na sakaki cikin kogin tinani wanda bazai bulle ba. Kuma na zabi nai miki magana ne yanzu saboda ina da tabbacin shine lokacin daya dace.

kitallafi rayuwata data tsunduma cikin tsananin soyayyarki, ki tausayawa zuciyar data shagala akan tsanananin soyayarki,kada rintsi ko zugar mahassada yasa ki gujeni ko kuma kirage son dakike mani.

Koma Karanta:  Shawara Ga Masoya da Samari Yan Soyayya

Ki sani: idan kika karbi Soyayya ta, zan kasance cikin farin ciki, zan saka ki farin ciki fiye da yadda kike a yanxu, zan gina miki fada ta qasaita a cikin Zuciyata wacce za kiyi Mulki Irin wanda kika so, zan shagwabaki, zan Baki Kula Dai dai Qarfina, zan baki komai na duniya indai inada damar mallakar shi, zan zamo miki Rumfa domin Kareki daga zafin rana, zan Zamo Lema agareki Domin Tare miki duk wata cutarwa, Bazan Sakaki Kuka ko Damuwa Ba, wannan Shine Alkawarina

Nasan Za kiyi Mamakin Yadda Akai na turo miki wannan sako, amma ba komai bane wannan idan Za’a kwatantashi da abunda zai biyo baya.

Ina neman wata kalma wadda babu wanda ya santa. Ina neman wata kalma da zan furta miki cewa…..ke ta daban ce, ke kyakkyawa ce, kin zarce sauran mata. Zuciya ta da taki ba za su ta6a rabuwa ba har abada. Ina son ki

Nasan wasu daga cikin halayyar ki, daya daga cikin shine bakya Wulaqanta mutane, wannan dalili yasa nace nima bari na gwada Sa’a ta ko Allah zai sa nayi nasara, dan Abun Sa’a ne.

Kullum ina Jaddada miki Kalmar INA SONKI Domin Wannan Kalmar itace Iyakar Qurewar Abunda Bakina Zai Iya Fada Akan Soyayyar ki, Duk Yawan Kalamai Duk Girman Bayanai, Duk Saukin Magana, Soyayya Ta agareki Bazata Iya Fassaruwa ba, da zaki Tsaga zuciyata Babu Abunda Zaki Gani Sai Gonar Danai Shukar Qaunarki, Cikin Jinina Kuwa Ba Komai Sai Ruhin Ki Da Yake Gudana Aciki. Ina Qaunar Ki Ne Da Raina Bada Bakina Ba, Ina Qaunarki Ne Da Zuciyata Bada Gangar Jikina Ba. Komai Naki Yayi Min.

SO shi ne abun da ya dun’kule zuciyoyinmu waje guda har muka tsinci kanmu a cikin soyayya, ina fatan ba za ki bari wani d’an ‘karamin abu ya zo ya raba tsakaninmu ba? Ina son ki. Ke tamkar gishiri ce a cikin rayuwa ta, idan na rasa ki zan yi rayuwa ne da babu armashi a cikinta. Ki Huta Lafiya.

Zanso mu Rayu Dake cikin Aminci, Zanso Na Kasance dake Cikin ko wani minti dake shudewa na rayuwata, zan So ki So ni fiye da yadda ni nake son ki, Bazan Miki Alkawarin Soyayya Har abada ba, amma na miki Alkawarin Zan Rike Soyayyar ki har zuwa Qarshen Nunfashi na, Da in rasa ki Shalelena Gwara Na Mutu banyi Aure ba, da Ace In Qare Rayuwata Babu Ke, na gwammaci Shan Guba Domin Rayuwata Babu Ke Tamkar Rayuwar Shukar Fure ne da Ba’ai mata Ban Ruwa.

Da akwai miliyoyin furanni a cikin lambun masoya a wannan duniya. Da a ce zan tsunko kowanne fure na baki shi a hannunki, hakan bai isa ya bayyanar da adadin yadda nake son ki ba. Ke ce murmushi na, kuma ke ce farin-ciki na. Ina Son Ki.

Na saka ki a zuciya tace badan kikai ba, sai dan kin Chanchanta, na shigo dake rayuwata ne badan Inaso ba, sai dan zuciyata tana Qaunarki, Na Bari Qaunarki Ta Kewaye Ruhin jikina ne saboda Ina Miki So na Gaskiya So irin wanda yafi na Uwa, so irin wanda bana Yaudara Ba, so irin wanda baki baya iya furtawa, Zan Iya Bada Duk abinda Na Mallaka Domin Na Mallakeki Jarumar mata.

Koma Karanta:  ALAMOMI 7 NA NUNA AN KAMU DA SOYAYYA

Da akwai wasu lokuta da nake zubar da hawaye saboda ke, na san za ki ce saboda me?…..Da akwai wani lokaci da yake zuwa na ji tamkar na yi fikafikai na tashi sama…..Kin kuwa san duk saboda mene ne? Saboda motsawar sonki a cikin zuciya ta da tsintar kaina a cikin matsanancin shau’ki a dukkan lokacin da na ji muryarki ko na tina da ke…..Ina fatan za ki amince mu rayu a tare har abada. Ina Son Ki!

Lokaci Mai tsawo na bata domin na fahimtar da zuciyarki soyayyata, kuma da duk kan alama hasashen zuciyata bai sabawa zahirinki Gimbiyata, Zuciyata da soyayyar ki na rene ta badan komai bah domin ki zame mata abokiyar rayuwa ta har abada, Koda jin sautin ki bazan iya yin nisa ba balle daga kallonki, Kamar Hasken farin wata haka nake hangen kyawun murmushin ki daga nesa domin ya kasance mai daukar hankalin mai kallo, Tabbas a zahirinki bazan iya misalta matsayin ki da komai bah saboda kamar furen fulawa haka kike da daukar hankali, Kowacce zuciya tana da nata burin ni tawa zuciyar kece muradinta

A lokacin da na samu soyayyarki sai na ji tamkar ni ne na fi kowa sa’a a duniya. A dukkan sanda na rintse idanuwa na sai na hango ni tare da ke muna tafiya a bisa gajimare. Idan na kwanta bacci sai na yi mafarkin mun zama mata da miji. Ina sonki, tare da son kasancewa a tare da ke har abada. Ki Huta Lafiya.

Amincin allah ya tabbata agareki hubby na adukkan lokacin da zuciyata zata harba jini kinanan acikin ta yakan harbawa ne tare d begenki, bazan taba dena tarairayarki ba a cikin zcyta ina qaunarki fiye da yadda uwa takeson Dan’ta , koda Yaushe kishirwan tunaninkice ta mamaye acikin zuciyata ke kadae kike da zumar da zats magance kishirwar dake acikin ruhina, aduniya jin muryanki ki shi me cireni aqunci kallon kyakkyawar fuskarki shine cikar burina, kinsace tunania kin kame dukkan wata kofar da take shiga da fice na bakin ciki dakeyin supply acikin rayuwata,wayyo qaunata nashiga tarkon soyayya nakamu da matsanancin begen yar fara, madaideciya ga farin idanu Allah yacika mun burina nakasancewa tare da me amatsayin miji da mata…

Sama cike take da taurari masu hasken da ke haske duniya a cikin kowanne dare. Amma haske mafi haskaka fuska da yaye duhun zuciya, na gan shi ne a cikin idanuwanki. Ki Kula Min Da Kanki. Ina Son ki.

Babu abin da zan iya boye miki tunda kin riga kin sani kuma kin fahimta da cewa zuciyana ta riga ta jefani cikin tarkon da bazan iya kubuta ba, Kamar yadda na jima ina sanar dake cewa sonki kullum yalwa yake a cikin zuciyata, yake kara karuwa tare da yaduwa babu ƙaƙƙautawa wanda a yanzu sun riga sunyi karfi da banida iko, ko kuma zabi wanda Ya wuce na bin umarnin zuciyata, wacce takasance tana mai yi min jagoranci zuwa ko ina a duniyar soyayyarki!

Wadannan Sune kalaman soyayya da Yakamata Masoya su Turawa Yan uwansu masoya, saboda soyayya sai an hada da kalamai.

Kuyi Register Sabon website namu https://lodachat.com

Rarraba

2 thoughts on “Kalaman Soyayya Masu Dadi da Ratsa jiki:- Soyayya”

Leave a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Open chat
1
Barka Da Zuwa 👋 kana son yin Register da sabon website dinmu

Kana da Bukata?
%d bloggers like this: