kalaman soyayya masu ratsa jiki- Domin Masoya

Rarraba

Ga wasu kalaman soyayya masu ratsa jiki, dadadan kalaman soyayya, kalaman soyayya masu dadi gasket, kalaman soyayya da kauna, kalaman soyayya masu zafi.


Yabo da Jinjina Zai tabbata gareki diyar kirki, duk wata fata na Alkhairi Dole nai miki shi, kin zaburar da Zuciya Ta daga dogon suma na rashin irin ki a rayuwata,

Zuciyata Ta Aminta Da Kalaman Ki Domin suna saka ni farin ciki, HubbyNa kece Abu mafi Dandanon Zaki mai canja tinani acikin rayuwata, tankaden DA nayi dakuma Reraya, Naga Ribar Shi Akan ki, HabibiNa Ina Qaunar ki da Zuciyata dakuma Raina,

Zan Cigaba da Qaunar ki Har Zuwa Ranar Dana Daina Numfashi, Sahibata Ina Son Ki,

Soyayyar ki ta rufe min idanu Bana Son Naji ko a Mafarki Labarin Soyayyar wata ɗiya Mace Sai naki HubbyNa,

Koma Karanta:  Matakai na Yadda Zaka Sace Zuciyar Wadda kake so Ba tareda kace kana sonta ba

Samun ki Sa’a ce garen Babba Matata, Daga Karshe ina Fatan Sahibar Ruhina Tana cikin Qoshin Lafiya. Sannan Ina Fatan kina Cikin Farin Ciki. Ina Qaunar Ki.

Zuciya ta tana ta faman jirankI burinta kawai ta gankI sannan idanuwa na sun kasa ganin kowa ba abin da suke son gani sai kykyawar fuskar kI abin alfaharina Kaunar ki ta mamaye mini Dukkannin sassan ilahirin jikina.

Assalamu alaiki farin cikin zuciya ta kuma sanyi idanuwana, hakika kece mace ta farko wacce na yi gamo da ita,

bantaba zato ko tsammanin za’ayi wata ‘ya mace wacce zata sace min dukkanin ruhi a mafi kankantar lokaci ba sai ke,

amma sai gashi ba tsammani nayi kicibis da kyakkyawar fuskar da na kasa dauke wa kallo,

Hakika kyauwun ki yakai ayi misali dashi, kinsha gaban duk mai tinani, zuciyar ki Kyakkyawa ce, tafiyar ki mai tsari ne,

Rayuwar ki abar kallo da koyi ne, lallai nayo matukar Sa’ar samun mace kamar ki a cikin rayuwata Muradina, Annuri na, Kuma Shalelen Zuciyata.

Zabin Raina kece daya tilo, Bani da kamar ki a zuciyata, tsananin Qaunar da nake miki zuciyata ce kawai take iya dauka bakina kamantawa kawai yake, kina sani farin ciki,

Koma Karanta:  Samfurin kalaman Soyayya na biyu 2

shigowarki cikin rayuwata Ya saitamin abubuwa da dama, Dani dake rabuwar mu sai Allah,

babu wata diya mace mai Zakin baki ko dadin murya ko kyawun jiki kona fuska, iya tafiya ko kwarji da zata daukemin hankali akan ki,

Ke din dai kece, kece Badadayata Dake zanyi rayuwa bana son kowa sai ke. Idan da rai Zaki zamo matata,

niko zan zamo miki miji, zamuyi rayuwa mai dadi, zan debe miki kewa zan saka ki farin ciki iya iyawata, Zan Baki Duk Abunda Kike so.

sonki yayi mini da baibiya yabi jini, tsoka, zuwa bargon kashina. Domin zuciyata ita ce ma’adanin surrikan tinaninki

HubbyNa Zan kasance dake a zuciyata Ba tare da wata fargaba ba, zan killace Soyayyar ki araina. Duk Ranar Da Nace Miki Bana sonki To Bani bane Saidai wanina,

Inason muyi zama na amana, mu baiwa junan mu girma, kada musa raini a lamarin mu domin cigaban farin cikin mu muyi so dan Allah Na Gaskiya.

abin da zuciya take so ta samu a wurinki wannan yasa da Na zauna ina tunanin ki kawai na ga hawaye Na zuba daga cikin ida nuwana.

Koma Karanta:  Soyayya Zallah: Karanta Yadda Alamomin So (Soyayya) Suke

Kyakkyawar zuciya tana rayuwa ne qarqashin inuwar aminci, da amincewa, zuciyar da aka cudanyata da tsarkakekkiyar soyayya tana Samar da ingantacciyar lafiya agangar jikin ma’mallakinta,

Haqiqa zuciya kalmace tamusanman don soyayya, soyayya kalmace ta musanmace don kulawa, ita kuma kulawa kalmace ta musanman domin ke,

ke ta musamman ce agare ni… Ina yiwa Allah godiya dayabani nagarcecciyar mace irinki. My unforgettable.

Na kasance ma’abocin soyayya zuciyata ma ta gaskata hakan, Lokaci na shudewa soyayyarki na karuwa a cikin zuciyata,

A lokacin da ki ke cikin farin ciki kyakkyawar fuskar ki na bayyanar da murmushi mai taushi da tausa sa zuciyar ma’abocin kallonta, kece wadda na ke so a cikin zuciyata babu wata da za ta iya canja matsayin ki a wajena.

Domin Samun Sababbin shiraruwan mu Na Musamman kuyi Register Yanzu a website namu

https://lodachat.com

Rarraba

17 thoughts on “kalaman soyayya masu ratsa jiki- Domin Masoya”

  1. Na rasa Mace maiSONA tsakani da Allah.
    Idan akwai ga number na pls; 08087880402

    Idan na iya kalaman SO Banda budurwa miye amfanin?

  2. Jikan sarki kazaure

    Rana da wata basa gushewa kullum to haka sonki take yawo zuciya ta idan har kika ga sonki ya daina yawo to tabbas babu rana babu wata .

Leave a Comment

Your email address will not be published.

Open chat
1
Barka Da Zuwa 👋 kana son yin Register da sabon website dinmu

Kana da Bukata?
%d bloggers like this: