Tsaya Kajiya!! Karanta Kalaman soyayya Masu Ratsa Zuciyar masoya- Shiga Yanzu

Rarraba

Wadanna kalaman soyayya masu ratsa Zuciyar masoya Wasu nau’in kalamai ne sababbi na daban Domin masoya.

Insha Allah zamu cigaba da kawo muku kalaman soyayya irinsu.

  • Kalaman bada Hakuri a Soyayya.

  • Kalaman soyayya Da turanci

  • Kalaman soyayya apps (Zamuyi apps na android zamu Sa kalaman aciki.

  • Kalaman ban Hakuri a soyayya

  • Kalaman soyayya da da da

  • Kalaman soyayya na hausa

KIN ZARCE SAURAN MATA.

SINADARIN RAYUWA TA.

SO shi ne abun da ya dun’kule zuciyoyinmu waje guda har muka tsinci kanmu a cikin soyayya, ina fatan ba za ki bari wani d’an ‘karamin abu ya zo ya raba tsakaninmu ba? Ina son ki. Ke tamkar gishiri ce a cikin rayuwa ta, idan na rasa ki zan yi rayuwa ne da babu armashi a cikinta. Ki Huta Lafiya.

Koma Karanta:  Mata Zallah: Kalaman soyayya masu ratsa jiki (Na Mata) Zallah

ZAN SO KI JI.

Da akwai wasu tarin tsintsaye da suke wuni suna tattauna batutuwa a kan irin matsayin da na baki a cikin zuciya ta. Zan so ki ji irin abun da suke cewa, domin kuwa a lokacin ne za ki tabbatar da irin son da nake yi miki. Ina Son Ki!

KE CE MURMUSHI NA.

Da akwai miliyoyin furanni a cikin lambun masoya a wannan duniya. Da a ce zan tsunko kowanne fure na baki shi a hannunki, hakan bai isa ya bayyanar da adadin yadda nake son ki ba. Ke ce murmushi na, kuma ke ce farin-ciki na. Ina Son Ki.

SONKI NA MOTSAWA A ZUCIYA TA.

Da akwai wasu lokuta da nake zubar da hawaye saboda ke, na san za ki ce saboda me?…..Da akwai wani lokaci da yake zuwa na ji tamkar na yi fikafikai na tashi sama…..Kin kuwa san duk saboda mene ne? Saboda motsawar sonki a cikin zuciya ta da tsintar kaina a cikin matsanancin shau’ki a dukkan lokacin da na ji muryarki ko na tina da ke…..Ina fatan za ki amince mu rayu a tare har abada. Ina Son Ki!

Koma Karanta:  Wasikun Soyayya: Samfurin kalaman Soyayya Ga Masoya

HMM!! KI YARDA DA NI.

A dukkan lokacin da dare ya yi, ki d’aga kanki sama ki kalli sararin samaniya, za ki ga wani tauraro yana saukowa izuwa gare ki, karda ki yi mamakin me ya sa haka ya faru? Ki yarda da ni, hakan zai iya faruwa a zahiri domin kuwa ni ma na yi hakan har ta kai ga na same ki. Hmm! Ki Huta Lafiya.

INA SON KASAN

CEWA A TARE DA KE HAR ABADA.

A lokacin da na samu soyayyarki sai na ji tamkar ni ne na fi kowa sa’a a duniya. A dukkan sanda na rintse idanuwa na sai na hango ni tare da ke muna tafiya a bisa gajimare. Idan na kwanta bacci sai na yi mafarkin mun zama mata da miji. Ina sonki, tare da son kasancewa a tare da ke har abada. Ki Huta Lafiya.

A CIKIN IDANUWANKI AKWAI WANI SIRRI.

Sama cike take da taurari masu hasken da ke haske duniya a cikin kowanne dare. Amma haske mafi haskaka fuska da yaye duhun zuciya, na gan shi ne a cikin idanuwanki. Ki Kula Min Da Kanki. Ina Son ki.

Koma Karanta:  Soyayya: Cigaban kalaman Soyayya Domin Masoya

HARSHEN ZUCIYA.

Furanni na furta kalmomin yabo a kanki a dukkan lokacin da na shiga lambu mai d’auke da ‘korama gami da korayen ciyayi da bishiyu masu d’auke da tsintsaye. Sukan rera baitukan yabo a gare ki, cikin harshen da zuciya ce kawai ke iya fahimtarsa. Ina Son Ki.

BA ZAN IYA RAYUWA IDAN BA TARE DA KE BA.

A mafarki da kuma a cikin soyayya babu abun da ba zai iya faruwa ba. Ina son ki sosai hakan ya sa nake ji tamkar ba zan iya rayuwa idan ba tare da ke ba. Ba na fatan rasa ki a rayuwa ta, domin kuwa a dukkan lokacin da na rasa ki, na tabbatar da rayuwa ta za ta shiga garari. Ina Son Ki kuma ba zan ta6a canjawa a kan hakan ba.

Kada kamance kadan Yi sharing zuwa Ga wasu. Mungode. 🙏🙏

Rarraba

Leave a Comment

Your email address will not be published.

Open chat
1
Barka Da Zuwa 👋 kana son yin Register da sabon website dinmu

Kana da Bukata?