Kalaman soyayya Masu ratsa Zukata, Jiki Da jinin Masoya Na (2022)

Rarraba

Hak’ik’a nayi dace da samun kyakkyawar mace abar kwatance. Zan kasance tare dake a duk inda kike, cikin mafarkinki, cikin tunaninki, cikin farinciki da bak’in ciki.

Zan kasance mai share maki hawayen ki, ya ma za’ai in bar idanuwanki su zubar da hawaye ?

Zan kasance mai tarairayar ki tamkar kwai a tafin hannu.

Fata na ki kasance cikin farin ciki da annashuwa, fata na ki zamto tauraruwar dake haske duniyar masoya. Ke ce tawa har abada, ki huta lafiya.

kamar yadda taurari ke yin haske gamida kyalli a sararin samaniya. To haka fuskanki take haske gami da kyalli a cikin zuciyata.

ba zan iya rayuwa daidai da minti dayaba ba tare da ke ba., saboda kece kadai a rayuwata ina sonki. Ina kaunar ki gimbiya ta kece masoyiyata ta hakika a cikin wan nan duniyar, ina sonki na ne har abada.

ko alama ba zan iya mantawa da keba saboda cigaba da kaunarki abune mara gushewa ina sonkine fiye da yadda nake son kaina.

ina sonki ne fiye da yadda kike tunani ina sonki san nan kuma a shirye nake da na mutu a kanki

bani da wani abuda zan tuna a koda yau she fiye da ke.

kowane irin ma tsayi zan fuskanta a rayuwata koyaya jama’a zasu tsaneni, yake zuman raina koda me mutane zasu kirani. To kuwa zan kara farashin soyayyata a gareki

zan cigaba da sonki. Kuma zan nuna miki soyayyata a gareki tsarkakakkiya ce.
nayi imani cewa ”soyayyarmu ta hakikace” ba a binda zai sanya in daina sonki har a bada komai tsa nani komai wuyaâ.

Na dade ina kallon taurarin samaniya yayinda naga wacce tafi kowacce haske, saina naga bakowa bace nike ganiba sai ke masoyiyata!

So gamon jinine, haqiqa sonki ya zamo jinin jikina!

Kinfita daban a cikin mata, duk lokacin da na kallleki, sai naga kamar babu kyakykyawar wace sai ke!

Ki kwantar da hankalinki masoyiyata babu wata a zuciyata sai ke kadai!

Yarda da amincewarki gareni, sune zasu tabbatar da soyayyarki tagaskiya a gareni!

Farin ciki baya dorewa a rayuwa sai tare da bakin ciki, dan haka kowane hali nike bazan ta6a mantawa dake ba masoyiyata!

Nakan raba dare ina mai roqon Allah don neman biyan buqata, ko kinsan kece abu na farko da nike roqo samu!

Yanayin sanyi kan sa mutum ya takura, tare da lullu6a da qaton mayafi amma ni duk sanyin da ake idan na tunaki sai naji tamkar yanayin zafi!

Kamar yadda kowacce bishiya kanyi rassa a sama, kuma tayi saiwa a qasa, haka sonki ya mamaye dukkan jikina, idan na kalleki sai nayi farin ciki, idan naji tattausan muryarki, sai nishadi da walwala tare da annashuwa gami da farin ciki su mamaye zuciyata!

Tabbas Furanni suna da ‘kamshi, Zuma kuma tana da za’ki launin ciyawa kuma kore ne, amma ke babu wata kalma da zata iya bayyanar da zahirin siffarki sai dai kawai na ce ke kyakkyawa ce. Ina soki.


Zuciyarki ta zama takarda, tawa ta zama biro in rubata miki shafin kauna !

Kizama kofa na zamao makulli, mu hadu mu bude kofar soyyar lambun zuciyata!

Na kasa tsaye na kasa zaune a lokacin da na fara ganin ki a cikin taro , kin fita daban kaman wata a daren sha biyar!

Watau yau da na tashi, sai na ga rana ta taso ta haske garin nan, amma duk hasken ta ba kai hasken fuskar da haske zuciyata, domin ni a zuciyata Hasken fuskar abun quana ta yafi duk hasken raina.

Ki zama petur na zama inji mu hadu mu ta da lantarkin qauna ya shiba ta na baki filin zuciya ta ki shuka a duk wani lungun da sako bushiyar so a kauna don mu sami inuwar da zamu zauna muyi soyayya.

Kece madubi abar dubawata duk safiya, kin zamo min tamkar fetur a mota, rayuwata ba ke lami ce ya rabin raina.

Ke ce makwarariyar madarar zuciyata, wadda da na sha za ta haskaka zuciyata tayi fari.

Rayuwata babu ke tamkar wayar da ba wayar chaji ce, kuma babu layi, a mace ba amfani.

Kunne ya kurmance saboda rashin jin kallamen quanar ki kullum, baki ya daina magana dai dai saboda rashin begen zumar rayuwata kullum.
ya tsagwaron zallar tsabar kwayar tsokar zuciyata, idona zai makance saboda rashin ganinki a yau da kullum Ya gangariyar madarar zumar da bata da gauraye,

ya tauraruwa a cikin jinsin taurari mai haske zuciyar masoyinta. Idona ya bude ya ga haske irin na walkiya don ya gan ki.

Zuciyata na shan lawgadar zuma da madarar kauna Idon basira lafazin rayuwata.

Alfijir na qauna ya keto, tsuntsayen soyayya sun tashi su na yayo a sararin samaniyar zuciyata Ya fankar da ke juya zuciyata.

zan zamo kwale kwale ki shigo mu hau kan kogin so, in zamo katifa ki zamo gado a cikin dakin kauna.

Hadarin begen ki ya hado, guguwar sonki ta taso, sai ruwa mai karfi ake yi na kaunar ki a filin zuciyata.

Gaisuwa daga kamfanin so, har abar kauna, gida mai lambar zuciyata layin begen ki, zuwa ga rabin rayuwata.

ya zare da allurar da ta dinken zuciya ta, bazan taba daina sonki ba har sai wutar lantarki ta zauna a nijeriya. .

ya majaujawar zuciya ta, zan zama guga ki zama igiya mu hadu a jefa mu cikin rijiyar soyayya.

Ya tsokar zuciya ta, zan so ace ki zama fura in zama nono mu hadu a kwaryar soyayya.
Ya sahiba ta ki zama fukafikin dama in zama na hagu mu hadu mu ta da tsuntsun soyayya.

Ya masoyiyata, ki zamo bishiya in zamo ruwan da zai ratsa ta kasar so ba dan kome ba sai dan in shayar da ke.

Ya masoyiyata, ki zamo hanta in zamo jini, muga mai raba mu. Ludayin kaunar ki kin mamaye min kokon zuciyata. Ya masoyiyata, ki zamo mai in zamo alabasa mu hadu mu soye juna.’.

masoyiyata, ki zama candir in zamo ashana, ku zamo itace in zamo makamahi mu hura wutar so, domin mu tafasa tukunyar kauna.

Ya madarar zuciyata, ki zamo ciminti in zamo bulo mu gina gidan qauna a filin soyayya
Koma Karanta:  Soyayya: Yadda Zaka Ci Riba A Soyayya

IDAN KIKA RABU DA NI ZAN SHIGA HA’DARI.


Son ki a cikin zuciyata tamkar numfashi ne da yake futa daga hancina wanda tsayar da shi dai-dai yake da mutuwata, idan haka ne tayaya kike ganin zan iya futar da son ki daga cikin zuciyata? Ina son ki ma’abociyar kyawu. Ki huta lafiya.

Hausafamily na godiya.

Rarraba

1 thought on “Kalaman soyayya Masu ratsa Zukata, Jiki Da jinin Masoya Na (2022)”

Leave a Comment

Your email address will not be published.

Open chat
1
Barka Da Zuwa 👋 kana son yin Register da sabon website dinmu

Kana da Bukata?
%d bloggers like this: