KARANTA HUKUNCE-HUKUNCEN AZUMI NA SHEIKH BIN BAZ:

Rarraba
Budin Baki a Ramadan

Na farko:
Goge baki da brush da macklin baya karya azumi kamar yadda amfani da asuwaki baya lalata azumi.
Amma saiya rika taka tsan-tsan dan kada yawuce cikinsa, amma idan wani abu yawuce masa bada gangan ba to babu ramako akansa.
Hakama digon ruwan da na kunne basa lalata azumi cikin zance mafi inganci na malamai.

Na biyu:
Duk wanda amai yagalabceshi babu ramako akansa, amma idan shi ya kwakulo aman da gangan to azuminsa ya lalace saiya rama.

Na uku:
Ya halatta ayi amfani da ruwan turare kamar man itace harma da turaren wuta da rana cikin Ramadan.

Na hudu:
Haramun ne kallon mata, idan kuma kallon yazama da nufin sha’awa to haramcin yafi tsanani, amma kuma kallon baya lalata azumi sai in yakai ga fitowar maniyyi.

Na biyar:
Yawu baya bata azumi sabida haka don mutum ya hadiyi yawu ba laifi.

ALLAAH YAKAWO MANA KARSHEN ANNOBAR COVID-19.

Abu Habibillah Abdallah Mustapha Assalafiy Biu.

Rarraba

Leave a Comment

Your email address will not be published.

Open chat
1
Barka Da Zuwa 👋 kana son yin Register da sabon website dinmu

Kana da Bukata?