Maganin Gyambon Ciki (Ulcer) Cikin Sauki
Wannan Wani Nau’ine Na Maganin Gyambon Ciki .
Akwanan baya mun kawo muku Wasu daga cikin Maganin ta (Ulcer) to yau ga wata sabuwar hanyar
Ko kana/kina fama da cutar gyambon ciki (ulcer)??

MAHADI
- Garin habbatu sauda (babban cokali 6)
- Garin hulba (babban cokali 6)
- Zuma (kofi daya)
A zuba a mazubi daya sai a gauraya su.
Za a sha maganin cokali uku (safe, rana, dare).
Abin lura: da safe za’a sha maganin ne kafin aci abinci sannan bayan an sha baza’a ci abinci ba har na tsohon awa daya.
Hakama da rana bayan an sha maganin baza’a aci abinci ba sai bayan awa daya. Da dadare kowa za’a sha bayan cin abinci kafin kwanciya barci.
Allah yaba kowa Lafiya Ameen