Mata Zallah: Kalaman soyayya masu ratsa jiki (Na Mata) Zallah

Rarraba

Mata Zallah: Kalaman soyayya masu ratsa jiki (Na Mata) Zallah

To zanyi rubutu akan wannan dalilai zasu iya Kai dalilai biyar 5 zuwa shida 6.

Zan fadi guda daga cikin su yanzu Amma ba tare da nayi bayani ba, bayani Sai nayi rubutu nan gaba.

Dalili na Daya shine “Karancin iya soyayya “

Yi tunani Dan uwa, kana Da ra’ayi akan wannan rubutun Da zanyi nan gaba to Yi comment kasa.

Koma Karanta:  SOYAYYA ZALLAH; SAKONNIN SOYAYYA 18 NA BARKA DA SHAN RUWA NA MAZA

Kai tsaye ga kalaman nan a kasa.

INA SONKA MASOYI NA!

Tsuntsaye na bu’katar fukafukai domin tashi, kifi na bu’katar ruwa domin ya yi rayuwa, ni kuma ina bu’katarka domin na yi rayuwar farin-ciki. Ina son ka masoyi na!

MU KASANCE A TARE.

Ina son jinka a kusa da ni, ta yadda numfashi na da naka zasu gauraya, ta yadda zan ke juyo sautin bugun zuciyoyinmu na fita a tare. Mu kasance a tare har abada. Ina Son Ka!

INA FATAN MAFARKI NA YA ZAMA GASKIYA.

Koma Karanta:  Matakai na Yadda Zaka Sace Zuciyar Wadda kake so Ba tareda kace kana sonta ba

A kullum na kwanta bacci, na kan yi mafarkin ka zama uban ‘ya’ya na, ni kuma na zama mata a gare ka. Sai dai na san iya mafarki ba zai wadatar da ni ba a bisa kulawar da nake tinanin samu daga wajenka. A saboda haka nake fatan mafarki na ya zama gaskiya watarana. Ina Son Ka!

MASOYI NA.

Ina Son Ka, zan kuma ci-gaba da sonka tun daga futowar rana har izuwa fad’uwarta a cikin kowace rana har abada. Ka Huta Lafiya.

KA ZAMA RUHI NA.

Koma Karanta:  Samfurin kalaman Soyayya na biyu 2

Ina fatan ka fahimci manufa ta? ina fatan ka gane nufi na a kanka? Zan rayu ne cikin sonka har zuwa ranar ‘karshe, saboda kai ba saurayi ne kawai a waje na ba, ka zama ruhi na, sonka na yawo ne a cikin jinin da ke gudana a jiki na. Ina Son Ka!

Idan Akwai mai ra’ayi a kan Wannan rubutun Da zanyi nan gaba to Yi Yi comment kasa.

Muna Godiya.

Rarraba

1 thought on “Mata Zallah: Kalaman soyayya masu ratsa jiki (Na Mata) Zallah”

Leave a Comment

Your email address will not be published.

Open chat
1
Barka Da Zuwa 👋 kana son yin Register da sabon website dinmu

Kana da Bukata?
%d bloggers like this: