NISHADI: GA WANI SABON SAMFURI KU ZO KU KOYA.

Rarraba

NISHADI: GA WANI SABON SAMFURI KU ZO KU KOYA.

Jiya Ina Sauraren Wani Shiri A Wani Gidan Radio A Kano.

Naji Wani Sabon Al’amari, Wai Wani Magidanci ne Matarsa Ta Haihu

Ranar Suna Ya Gayyato Abokinsa Ya Tayashi Tatsar Hanji Da Suyar Ragon Suna.

A gaban Danginsa Dana Maijego.

Haka Ya Yini Yana Suya, Sai da Ya Gama Tsaf Ya Raba Naman Kaso hudu,

kaso 1 Nashi ,

kaso 1 Na Maijego

Sai Kaso 1 Na Iyayensa Ko Gidansu

Sannan Ragowar Kaso 1 Na Iyayen Maijegon.

Koma Karanta:  Musha Dariya Dole, Labarin Jika Da Kakansa

A Hirarsa Da Yan Jarida, Yace Haihuwar Matarsa Ta Farko Rago Da Tunkiya Ya Yanka,

Amma A karshe A Farar Leda Karama Aka Ba shi Kasansa.

Shiyasa Wannan Karan Yayi Komai Da Kansa.

Ita kwa Maijego Tace Nama Yayi Dadi Ya Soyu Yanda Akeso.

Akarshe Ya Shawarci Mazaje Suyi Koyi Da Dabarunsa,

Su Aje Kunya Da Ganda Saboda Dangin Maijego Yawanci Suna Suya Suke Cinye Rabin Naman Sunan Da Sunan Dandane.

Zaka iya haka?

Rarraba

Leave a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Open chat
1
Barka Da Zuwa 👋 kana son yin Register da sabon website dinmu

Kana da Bukata?