SOYAYYA ZALLAH; SAKONNIN SOYAYYA 18 NA BARKA DA SHAN RUWA NA MAZA

Rarraba

SAKONNIN SOYAYYA 18 NA BARKA DA SHAN RUWA NA MAZA

2} Kasancewar ki a tare da ni, ya sa ni jin kaina a matsayin wani mutum mai daraja ta musamman. Ina son ki, so irin wanda kalmomi ba zasu iya bayyanawa ba. Barka Da Shan-ruwa.

3} Na kasance cikin murnar zagayowar watarana, wato ranar da kika nuna amincewarki ga soyayyata. Ba na jin zan iya rayuwa ba tare da ke ba, saboda ke ce rayuwata, kuma ke ce mahaÉ—in numfashin da nake shaka. Barka Da Hutawa.

4} Na kan yi mamaki a baya, a duk
lokacin da na ga wani ya shiga
matsananciyar damuwa a kan so, amma bayan haÉ—uwata da ke, na fahimci abin da ake kira da so. A halin yanzu, ni ma a shirye nake da na yi yaki da duk wanda ya yi kokarin raba ni da ke. Barka Da Shan-ruwa.

5} Matukar zan cigaba da kasancewa a tare da ke, ba na jin hatsarin da nake ji ana cewa so yana da shi zan gamu da shi watarana. Ke ta daban ce kuma ta musamman a cikin rayuwata. Ina Son Ki.

Koma Karanta:  SOYAYYA MAI DAÆŠIN GASKE GA MASOYA

6} Kamar yadda zai yi wuya mutum ya manta da wani É“angare na jikinsa, haka ni ma zai yi wuya na manta da ke a rayuwata. Kin shiga zuciyata kin zauna, kin bi jijiyoyin jikina kin narke a cikin jinina. Ina Son Ki. Barka Da Shan-ruwa.

7} Burina a yanzu, bai wuce ganin na
mallaki tauraruwar da haskenta ke haske sararin samaniya ba, a kowane dare. Wadda nake fatan ta haskake rayuwata da haske mara disashewa. Ke ce dai wannan É—in nan, wadda ke bayyana a cikin baccina, ko a lokacin da nake farke, da rana ko a cikin dare. Ina Son Ki.

8} Fatana a ko da yaushe, na gan ki cikin walwala da nishaɗi. Burina na ga fuskarki cike da fara’a da annushuwa. Fatan Kin Sha-ruwa Lafiya.

9} Ki kalli sararin samaniya, za ki gan ni tsaye a kusa da ke, domin kuwa, ni ma na yi hakan kuma na gan ki a kusa da ni, haskenmu na haska duniya. Ina Fatan Kin Sha-ruwa Lafiya? Na yi Kewar Ki.

10} Me zai hana ni kasancewa tare da
wadda ta mallaka min zuciyarta? Wadda nake da tabbaci kan yadda take gudun ganin na shiga damuwa? Wadda ke tattalin farin-cikina? Wadda sautin muryarta ke cire min kasala da sanya ni yin bacci mai cike da mafarkai masu daÉ—i? Ba kowa ba ce wannan face ke! Ina Son Ki. Barka Da Shan-ruwa.

Koma Karanta:  Kalaman Soyayya (Na DayEpisode 1- 4

11} A dukkan lokacin da muka yi nesa da juna, na kan ji da ma a ce akwai manyan tsaunika a kusa da ni, da na hau ko zan samu na hango murmushin fuskar nan taki mai taushi. Na Yi Kewar Ki.

12} Wasu na gulmar, wai watarana za a wayi gari na ji son ki ya ragu a cikin
zuciyata, idanuwana su daina ganin
kyawunki, ni kuwa na ce, ba na fatan
zuwan wannan rana ina mai numfashi a doron ‘kasa. Ni a kullum, ina jin sonki ne na karuwa a cikin zuciyata, a dukkan lokacin da muke tare ko muka nesanta da juna. Ina Son Ki.

13} Na ji tsoron mafarkin irin
mummunan halin da zan shiga a duk
lokacin da na rasa ki. Zamowa ta
cikakken mutum zai kammala ne a ranar da kika zama mata a gare ni. Ina Son Ki. Yaya Ibada?

14} HaÉ—uwarmu ta kasance ne bisa
kaddara, zamowar mu masoya ya faru ne bisa zaɓinmu, amma ba wa son ki gurbi a cikin zuciyata, ya zama dole ne a gare ni, saboda kin zamo wani ɓangare na rayuwata, haka kuma tinaninki ya zama masarrafin sarrafa akalar rayuwa da tinanina. Ina son ki, so irin wanda gangar jiki take yi wa ruhi. Barka Da Shan-ruwa.

15} Yunkurin sanin adadin yadda nake jin son ki a cikin zuciyata, da dalilan da suka saka nake kaunar ki, a gare ni, daidai yake da a ce na bayyana irin É—anÉ—anon da ruwa yake da shi ne a cikin baki. Tabbas abu ne mai matukar wahala. Fatan Kin Sha-ruwa Lafiya.

Koma Karanta:  Shawara Ga Masoya da Samari Yan Soyayya

16} Kina da dabaru na sanya ni yin
murmushi ko da a ce ina cikin fushi ne. Kin zamo wata ta-daban a gare ni. Ina son ki, so mara iyaka. Barka Da Hutawa.

17} Kina da kyau masoyiyata, fiye da
yanda kike gani a madubi. Kyawu ne irin wanda babu wani furuci ko zanen wani mai zane da zai iya fasalta shi. Ina Son Ki. Fatan Kin Sha-ruwa Lafiya.

18} Ina fatan mafarkin da na yi jiya, ya maimaita kansa a cikin baccina na yau, mafarkin da nake fatan ya zamo gaskiya, mafarki ne da a cikinsa na

Rarraba

1 thought on “SOYAYYA ZALLAH; SAKONNIN SOYAYYA 18 NA BARKA DA SHAN RUWA NA MAZA”

Leave a Comment

Your email address will not be published.

Open chat
1
Barka Da Zuwa 👋 kana son yin Register da sabon website dinmu

Kana da Bukata?
%d bloggers like this: